IDAN MUTUM YA RASA SALLAR JUMMA'A SAU UKU YA KAFIRTA?

عَنْ أَبِي الْجَعْدِ الضَّمْرِيِّ- وَكَانَتْ لَهُ صُحْبَةٌ- أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((مَنْ تَرَكَ ثَلاَثَ جُمَعٍ تَهَاوُنًا بِهَا طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ))

IDAN MUTUM YA RASA SALLAR JUMMA'A SAU UKU YA KAFIRTA?

IDAN MUTUM YA RASA SALLAR JUMMA'A SAU UKU YA KAFIRTA?

TAMBAYA

Assalamu alaikum, Allah shi gafarta mallam, shin wai idan mutun ya rasa sallar juma'a 3 ya zama kafiri?

AMSA

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Subhanallah! Wanda ya rasa sallar juma'a sau uku, da gangan, ba kuskure ba, yana sane, ba mantuwa ba, da zaɓi ko ganin daman sa, ba tilasci, toh bai kafirta ba. Amma Annabi yace duk wanda ya bar sallar juma'a uku yana mai sakaci da ita, Allah zai masa ɗaba'u (khatamu) a kan zuciyar sa, a nan duniya, ga hadisin 

 عَنْ أَبِي الْجَعْدِ الضَّمْرِيِّ- وَكَانَتْ لَهُ صُحْبَةٌ- أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((مَنْ تَرَكَ ثَلاَثَ جُمَعٍ تَهَاوُنًا بِهَا طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ)). 

Yana da kyau mu san menene ɗaba'u a wannan gaɓa. Ɗaba'u wata azaba ce ta kulle ko rufe kafar ji (kunnuwa) da fahimta (zuciya), ta yadda alkhairin dake wajen zuciya ba zai samu shiga cikin ta ba, haka kuma sharrin dake cikin ta ba zai fita daga cikin ta ba.

Ma'ana dai ɗaba'u, wata nau'in azaba ce a duniya dake sababin kai mutum halaka a nan duniya a lahira kuma gidan wuta, Allah ya tsare mu. Har ila yau ɗaba'u na kai mutum ga halaka ne saboda haifar masa da rashin fahimta, jahilci da son zuciya ba son gaskiya ba, har ta kai ga yana biyayya ga zuciyar sa ne ba ga Allah ko Manzo ba. 

Haka ɗaba'u na kai mutum ga munafunci kamar yadda alqur'ani yayi nuni a kai

(وَمِنۡهُم مَّن یَسۡتَمِعُ إِلَیۡكَ حَتَّىٰۤ إِذَا خَرَجُوا۟ مِنۡ عِندِكَ قَالُوا۟ لِلَّذِینَ أُوتُوا۟ ٱلۡعِلۡمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًاۚ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ ٱلَّذِینَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَٱتَّبَعُوۤا۟ أَهۡوَاۤءَهُمۡ)
[Surah Muhammad 16]

A taƙaice dai ɗaba'u, shine kuma khatamu, ciwon kafirci ne da Allah ke azabtar da kafirai da shi, Allah yana azabtar da musulmi da shi sai idan ya tuba, Allah yace

(أَفَرَءَیۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَـٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمࣲ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَـٰوَةࣰ فَمَن یَهۡدِیهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ)
[Surah Al-Jathiya 23]

Don haka wannan mutum ya gaggauta tuba da nadama, ya daina ƙin halartar juma'a don ya tsira, amma yana nan matsayin shi na musulmi bai kafirta ba. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 Amsawa:
Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Nature