HUKUNCE-HUKUNCEN JININ MACE MAI CIKI

Alal-Haƙiƙa Malamai sunyi Saɓani tun adacan harkuma yazuwa...

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ MACE MAI CIKI

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ MACE MAI CIKI

TAMBAYA:

Shin Mace Mai-Ciki zata iyayin Jinin-Al'ada ko batayi? Sannan a Shari'ance meye hukuncin wannan jinin in taga yazo mata?

AMSA:

Alal-Haƙiƙa Malamai sunyi Saɓani tun adacan harkuma yazuwa wannan zamani damuke cikinsa, dangane da hukuncin jinin da Mace Mai-Ciki zata gani, ansamu maganganun Malamai kamar Ƙauli-2 dangane da wannan Mas'ala:

(1)-Ƙauli nafarko shine, Malaman dake Mazhabin MALIKIYYA da SHAFI'IYYA, dakuma irin su
Shaykhul-Islam-Ibn-Taimiyya tareda Shaykh-Salihul-Usaimin, Sunaganin cewa Mace Mai-Ciki tana iyayin Jinin-Al'ada, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja dacewa antambayi A'isha-Matar-Mαиzoи Aʟʟαн( ﷺ ) cewa idan Mace Mai-Ciki taga jini ya zatayi? Sai tace zata dena Sallah harsai taga jinin yaɗauke, kuma sukace a Babin-Al'ada Mace tafi Namiji ƙwarewa aharkar domin ita daga jikinta jinin yake fita Saɓanin Namiji, Sannan kuma sukace A'isha tafaɗi wannan maganane agaban wasu daga cikin Sahabbai kuma babu wanda yayimata Inkari (musu) akan hakan, danhaka sukace idan Mace Mai-Ciki taga jini to indai har jinin yazo matane adaidai lokacin da tasaba Jinin-Al'ada yana zuwa mata Sannan kuma yayi adadin kwanakin da tasaba yanayi yaɗauke sukace to Jinin-Hailane, kokuma yakasance jinin yazone da irin Siffar Jinin-Haila kamar yadda Aηηαвι( ﷺ ) yake cewa:

" ﺇﻥ ﺩﻡَ ﺍﻟﺤﻴﺾ ﺃﺳﻮﺩ ﻳﻌﺮَﻑ "
MA'ANA:
Lallai Jinin-Haila baƙine kamar yadda akasanshi,

Danhaka Jinin-Haila yakanzo da Siffofi kamar haka: Launin-Baƙi-Baƙi, Mai-Kauri, Mai-Ƙarni, sannan kuma galibi Mace takanji wasu alamu kafin jinin yafita, danhaka kenan indai Mace taga waɗanna Siffofi to Jinin-Hailane yazo mata koda kuwa tana da ciki,

(2)-Ƙauli nabiyu kuma shine, Malaman dake Mazhabobin HANAFIYYA dakuma HANABILA da mafi yawa daga cikin Malamai Ahlul-Ilmi, suna ganin cewa babu yadda za'ayi ace Mace Mai-Ciki tayi Jinin-Haila, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wata ruwayar da'aka sake samu daga wajen ita A'isha ɗindai tana cewa idan Mace Mai-Ciki taga jini to kawai zataci gaba dayin Sallartane, Sai wannan yanuna cewa ashe Sahabbai basuyi Ijma'i akan wannan Mas'alarba kamar yadda wasu suka faɗa, Sannan suka sake kafa Hujja da Hadisin da Mαиzoи Aʟʟαн( ﷺ ) Yace da Umar-Ɗan-Kaɗɗab lokacin da ɗansa Abdullahi-Ɗan-Umar yasaki Matarsa tana cikin Jinin-Haila, sai Aηηαвι( ﷺ ) Yace da Umar-Ɗan-Kaɗɗab:

" ﻣﺮﻩ ﻓﻠﻴﺮﺍﺟﻌﻬﺎ ﺛﻢ ﻟﻴﻄﻠﻘﻬﺎ ﻃﺎﻫﺮﺍ ﺃﻭ ﺣﺎﻣﻼ ، "
MA'ANA:
(Yakai Umar) ka umarceshi (Abdullahi-Ɗan-Umar) dacewa yadawo da'ita (harsai tayi tsarki) Sannan daga baya inyaso sai yaketa (amatsayin) mai tsarki kokuma mai ciki:

Dakuma Hadisin da Aηηαвι( ﷺ ) Yake cewa:
" ﻻ ﺗُﻮﻃَﺄُ ﺣَﺎﻣِﻞٌ ﺣَﺘَّﻰ ﺗَﻀَﻊَ ، ﻭَﻻ ﻏَﻴْﺮُ ﺫَﺍﺕِ ﺣَﻤْﻞٍ ﺣَﺘَّﻰ ﺗَﺤِﻴﺾَ ﺣَﻴْﻀَﺔً، "
MA'ANA:
Ba'a saduwa da (baiwar da aka ribaceta awajen yaƙi) idan tana da ciki harsai in ta haife abindake cikinta, hakanan ba'a saduwa da (baiwar da akasayeta) wacce batada ciki harsai anjira tayi (istibra'i) da zuwan jinin haila sauɗaya:

Sannan kuma sukace Shari'a tasanya ayi Istibra'ine ta hanyar yin jini ɗaya, itakuma Idda ta hanyar yin tsarki-3, amma sai akace ita Mace Mai-Ciki Iddarta shine tahaife abindake cikintane kawai kamar yadda Aʟʟαн( ﷻ ) Yake cewa:

" ﻭَﺃُﻭﻟَﺎﺕُ ﺍﻟْﺄَﺣْﻤَﺎﻝِ ﺃَﺟَﻠُﻬُﻦَّ ﺃَﻥ ﻳَﻀَﻌْﻦَ ﺣَﻤْﻠَﻬُﻦَّ "
MA'ANA:
(Matan) dasuke da ciki sukuma Iddarsu shine lokacin dasuka haife abindake cikinsu:

Sannan kuma Malamai sukace ai Mace tana iya gane cewa tasamu cikine tahanyar yankewar Jinin-Hailarta, kuma da ace Mai-Ciki tana Jinin-Haila, to da itama sai yazama hukuncinta yazo daidai da waɗanda basu da ciki yayinda aka sakesu, kuma kowa yasani cewa idan akasaki Mace da ciki koda tayi Jini-3 bazai yiwu ace shikenan taƙare iddartaba, dole sai in ta haihaife abindake cikinta sannan taƙare Iddarta:

Bayagahaka kuma sukace asali dama jini yana fitowane daga mahaifar Mace a sakamakon cewa bakomai acikin mahaifar, to amma daga lokacin da Mace tasamu ciki gaba ɗaya wannan jinin antoshe masa wurin zamansa a mahaifar, kuma har ilayau wannan jinin shine za'amayar yazama abincin shi wannan Ɗan-Tayin dake cikin mahaifar ita.

Nature