WANE LOKACI NE DA MACE ME CIKI TAKE GAMA IDDA?

Amsa: Toh akan wannan matsalar malamai sunyi maganganu guda biyu.

WANE LOKACI NE DA MACE ME CIKI TAKE GAMA IDDA?

YAUSHE MACE ME CIKI TAKE GAMA IDDA

TABAYA

Idan miji ya saki matarsa tanada juna biyu tsawon wane lokaci ne iddarta zata kammala?

AMSA

Toh akan wannan matsalar malamai sunyi maganganu guda biyu. Ra'ayin farko shine abunda Mazhabar Malikiyya suka tafi akai wato zatayi idda da abunda suke cema Ab-adul ajalaini.

Wato sadda aka saketa se aduba aganin shin zata iya wuce wata uku bata haihuba? Idan zata iya wucewa toh haihuwarta shine iddarta.

Amma idan bazata wuce wata uku ba toh kota haihun bata gama idda ba harse ta cika watanni uku shine iddarta, wato su awajansu za'a duba agani shin tsakanin wata uku dakuma haihuwarta wannene yafi nisa? Duk wanda yafi nisa ɗin toh shine iddarta.

Amma wannan ra'ayine me rauni domin yasaɓama nassin Alƙur'ani da hadisi kuma mafi yawan malamai basuyi aiki dashiba. Abunda yake ingantacce shine kawai dazarar ta haihu shikenan ta gama idda koda kuwa aranarda ya saketa aranar ta haihu toh to idan tasamu wani mijin aranar ana iya ɗaura sabon aure babu wani wata ukunda za'a jira.

Hakama koda ace zata haura shekara bata haihuba toh iddarta baze ƙareba se sadda ta haihu wannan shine abunda Allah yafaɗa acikin suratuɗ ɗalaƙi kuma shine maganar mafi yawan malamai.

Allah Yasa mudace

Nature