MENENE HUKUNCIN SAKA AL-KUR’ANI A WAYA?
Amsa: Hakika wannan zamani ne na kimiyya da fasaha (technology)...

HUKUNCIN SAKA AL-KUR’ANI A WAYA
TAMBAYA
Yaya hukuncin saka Qur’ani a waya a musulunci? Akan kalli batsa a wayar, akan turo batsa baka sani ba ma, sannan kuma akan shiga bayi dashi. Ina neman Bayani game da Saka kur’ani a waya.
AMSA
Hakika wannan zamani ne na kimiyya da fasaha (technology), kimiyya ta mamaye komai, da alkhairinta ko sharrinta.
Daga cikin alkhairints akwai sanya Al-Kur’ani a cikin na’ura kamar wayar hannu. Yawaitar kimiyya yasa mutane na ta tambayoyi domin sanin Halal da Haram a cikin addinin mu. Ina rokon Allah da yakarama mai tambaya Ilimi, fahimta da dacewa akan kyakkyawan aiki.
Babu laifi a sanya Al-Kur’ani a na’ura mai kwakwalwa ( kamar waya, cassetes, CD/DVD plates, flash, computers etc).
Amma wajibi ne a tsare alfarmansa da darajarsa akan hakan.
Hukuncin mu’amala da batsa nanan akan Haramci, saidai baishafi Al-Kur’anin da ke cikin waya ba. Duk da cewa suna cikin waya ɗaya, to amma ko wanne yana mazauninsa.
Sai dai idan hakan yana taɓa darajar Al-Kur’anin da ke cikin wayar, to ayi gaggawan tsare martabar Al-Kur’ani, tahanyar kawar da batsar a cikin wayar. An tsinewa duk mai kallon tsiracin wani.
Makaruhi ne a shiga da wayar ko na’urar da ke ɗauke da Al-Kur’ani idan gilashin na’urar/wayar na buɗe da Al-Kur’anin kuma ana ganinsa a gilashin (screen). idan gilashin wayar baya nuna (displaying the text of Qur’an) ayoyin Al-Kur’ani a fili. Ko kuma wayar na kashe (swich off), ko tayi lumm da duhu ba’a ganin komai na Al-Kur’ani a gilashinta. To, idan gilashin wayar bai nuna Al-Kur’ani ba, babu komai.
WALLAHU A'ALAM

-
Zaneidu ben musaMaa Sha Allah
-
Muazu YusufMa sha Allahu Jazakallahu khairan
-
BnusmanAameen! Barakallahu feek.
-